20 Janairu 2022 - 10:08
​Shugaban Saliyo Ya Kori Ministan Shari'ar Kasar

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio ya sauke babban lauyan gwamnati kuma Ministan Shari'ar kasar, wato antoni janar daga mukaminsa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ba wani dalili da fadar shugaban kasar ta bayar kan dalilin sauke Anthony Yeiwoh Brewah daga aiki.

Sai dai kafofin yada labarai na kasar na danganta cirewar ga afuwar da aka yi wa fursunoni a ranar sabuwar shekara da kuma wani hoto da aka gani ministan ya dauka da wani daga cikin 'yan kason da aka saki.

Kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito cewa Mista Brewah yana cikin kwamitin da ya ba wa shugaban kasar shawarar yafe wa fursunoni 160.

Yanzu an maye gurbinsa da Mohamed Lamin Tarawalley.

342/